
Tashin hankali a wuraren hakar ma'adinai a Afirka ta Kudu
Tashin hankali na kara bazuwa a bangaren ma'adinai na kasar Afrika ta Kudu.
Yanzu haka dai an dakatar da aiki a ma'adanin Platinum na wasu Amurkawa.
Ma'aikatan kamfanin sun ce masu zanga zanga ne su ka yi masu barazana shi yasa su ka fice.
Dan siyasar Afrika ta Kudu, Julius Malema, a jiya Talata ya yi kira ga ma'aikatan ma'adinai a kasar, su kori shugabanninsu, saboda a cewar sa basa aiki yadda ya kamata.
A watan daya gabata ne yajin aiki a mahakar ma'aidinai a Marikana ta janyo tashin hankali, inda mutane fiye da 40 suka mutu, wanda yawancinsu 'yan sanda ne suka harbesu.


















