BBC navigation

A daina bai wa Rwanda tallafi - Human Rights Watch

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:24 GMT

Tambarin Human Rights Watch

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi kira ga kasashe masu bayar da tallafi da su sake nazari a kan gudunmawar da suke bai wa kasar Rwanda.

Kungiyar na zargin wasu dakarun sojin kasar da ci gaba da marawa 'yan tawaye baya.

Ana zargin 'yan tawayen da cin zarafin bil adama a makwabciyar kasar, Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, sai dai kasar Rwanda ta musanta cewa tana marawa 'yan tawayen baya.

A watan Yulin da ya gabata gwamnatin Birtaniya ta dakatar da gudunmawar da take bai wa kasar Rwanda, saboda tana zarginta da goyon bayan 'yan tawaye.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.