
Tambarin Amnesty International
Wani rahoto da kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta wallafa ya bayyana mawuyacin halin da mazauna gidan yari ke ciki a kasar Chadi.
Kungiyar ta ce wasu ma'aikatanta sun ziyarci gidajen yari shida inda suka gano cewa akwai cunkoson jama'a, inda a wasu lokutan yanayin zafi kan kai maki 48 a ma'aunin Celsius.
Kazalika kungiyar ta ce fursunonin ba sa samun isasshen abinci da ruwan sha, lamarin da ya sa suke fama da tamowa.
A cewarta, fursunonin na yin amfani ba makewayi guda da ba shi da cikakkiyar kulawa abin da ya sanya da dama daga cikinsu suka kamu da cututtuka.
Kungiyar Amnesty International ta kara da cewa maza da mata na kwana waje guda, kuma hakan na haifar da yanayi na cin zarafi tsakaninsu.
Ta yi kira ga hukumomin kasar su dauki kwararan matakai na inganta yanayin gidajen yarin.













