
Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce za a yi dukkan kokarin da ya wajaba na kamo wadanda suka kashe mutane hudun da aka tsinci gawarwakinsu a wani wurin shakatawa dake a wani gurin dake da tsaunika.
An samu gawarwaki uku a cikin mota a ranar laraba, kuma 'yan sanda sun yi imanin Iyali daya ne da suka fito daga Birtaniya.
Wasu majiyoyi sun ce direban sunan sa Sa'ad Al-Hilli wani Injiniyan na'ura mai kwakwalwa haifaffen Iraqi.
'Yan sanda sun gano 'yar ta sa ta biyu karkashin gawawwaki sa'oi da dama bayan kisan.
An kuma tsinci gawar wani Bafaranshe da kekensa a kusa da wurin.

















