
Sabon kakakin Majalisar Dokokin Somalia, Mohamed Osman Jawaar
Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane dari takwas ne su ka yi kaura daga garin Kismayo da ke kudancin kasar Somalia, a daidai loakcin da dakarun Kenya ke shirin kaddamar da wadansu hare-hare a garin.
A farkon makon nan ne sojojin ruwan Kenya suka yi luguden wuta a kan garin na Kismayo.
Na bayar da rahotn cewa sojojin na Kenya tare da hadin gwiwar wadansu sojojin as-kai sun dumfari garin na Kismayo.
Kisamayo ne dai gari na karshe mafi girma da kungiyar masu fafutukar Islama ta Al-shabaab ta mamaye.













