
Ranar 3 ga watan Yuni wani jirgin Dana Air ya yi hadari
Ministar sufurin jiragen sama ta Najeriya, Stela Odua, ta sanar da hujjojin da suka sa ma'aikatarta ta mayarwa kamfanin Dana Air lasisinsa don ya ci gaba da gudanar da harkokinsa.
Hakan kuwa na wakana ne bayan kwanaki casa’in da biyar da aukuwar hadarin wani jirgin sama na kamfanin na Dana Airline a Lagos da ke kudancin kasar, hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dari da hamsin.
Yayin wani taron manema labarai ne dai ministar, Uwargida Stela Odua, ta bayyana cewa:
Akwai sakamakon binkicen farko, akwai sakamakon bincike na karshe, kuma hukumar kula da kariyar sararin samaniya na ci gaba da gudanar da bincike.
Hakan kuma na cikin ka’idojin ayyukan jiragen sama—jirgin kamfanin jiragen sama na kasar Kenya ya yi hadari, jirgin kamfanin Air France ya yi hadari, haka ma jirgin kamfanin British Airline ya yi hadari, an samu asarar rayuka, amma kuma suna ci gaba da ayyuka ba a rufe kamfanonin ba.
Ta kuma kara da cewa, A sha'anin zirga-zirgar jirage, kariya na da muhimmanci; za a ci gaba da gyare-gyare da bunkasa al’amura.
A gaskiya mun ma yi abin da ba a taba yi ba da muka dakatar da su.
A halin yanzu dai kamfanin na Dana Airline zai ci gaba da daukar fasinjoji kamar yadda aka saba.
Sai dai fatan jama'a shi ne a ci gaba da bunkasa al’amuran zirga-zirgar jiragen sama kamar yadda suke a cikin kasashen duniya da su ka ci gaba, domin rage yawan hadura da ke lakume dubban rayukan jama'a.


















