
Sojin kasar Turkiyya na gudanar da aikin sintiri a kan iyakar Turkiyyar da Iraqi dake Lardin Sirnak.
Dakarun kasar Turkiyya kimanin tara ne suka hallaka a ricikin 'yan tawayen Kurdawa da ya abku a yankin Sirnak kamar yadda hukumomi suka bayyana, kana masu tada kayar baya kimanin 20 kuma aka hallaka a kusa da kan iyakar kasar Syria da Iraki.
Fadan dai ya rincabe ne da tsakar daren Lahadi, kuma ana ci gaba da gwabza wa.
Rikicin tsakanin jami'an soji da mayakan 'yan tawayen Kurdawa na PKK, wadanda suke neman 'yancin cin gashin kai ya kara kazanta a yankin cikin shekara guda.
Kafar yada labarai ta kasar Turkiyya ta ce mayakan 'yan tawayen na PKK sun kai hari da bindigogi da rokoki kan harabar sansanin soji a garin Beytussebap a daren Lahadi, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar jami'an tsaro takwas.
An dai dora alhakin kazancewar rikicin a cikin watannin baya-bayan nan kan fadan da ke faruwa a makwabciyarta kasar Syria.













