
Sabon wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Lakhdar Brahimi
Sabon wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria, Lakhdar Brahimi, ya ce aikin da ke gabansa tamkar wani abu ne mai kamar da wuya.
Yayin da ya ke magana da BBC bayan ya karbi mukamin na sa, Mr Brahimi ya yi amannar jin tsoron nauyin da ya rataya a wuyansa, yana mai cewa kasashen waje ba sa tabuka wani abin ku zo ku gani wajen hana yawan mutuwar da 'yan kasar Syria ke yi.
Kofi Annan, wanda ya gabaci Mr Brahimi, ya sauka daga mukaminsa a cikin watan Agusta, bayan da rikicin da ke tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye ya kara ta'azzara, wanda kuma ya kasance dukkannin bangarorin biyu suka nuna turjiya game da shirinsa na wanzar da zaman lafiya.
Mr Brahimin dai ya nuna karayarsa game da aikin da ke gabansa na tunkarar rikicin kasar ta Syria.
'' Ina mai matukar tsoron girma da nauyin aikin da ke gaba na, mutane suna ta fadin cewa mutane na mutuwa, me za ka yi domin taimakawa? Kuma a gaskiya ba ma yin wani abin ku zo ku gani, ko wannan ma ai wani babban abu ne, dole ne a ji tsoron lamarin."
Mutane da dama ne musaamman fararen hula a Syriyar ke ci gaba da rasa rayukan su, sakamakon kara kazancewar da rikicikin ke yi tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a kasar.












