
Masu zanga-zanga kan dokar aikata sabo a Pakistan
Hukumomi a kasar Pakistan sun tsare wani limamin addinin Musulunci da ya zargi wata yarinya kirista mai kimanin shekaru goma sha hudu da aikata sabo.
An kame Limamin ne bayan da wani mutum da ya gabatar da shaida a gaban wata kotun Majistare ya ce yaga lokacin da limamin Khalid Chishti, ke dasa wasu fallayen alkur'ani mai tsarki tare da wasu takardu da aka kona a jakar yarinyar.
Daga bisani dai an zargi wannan yarinyar ce da laifin kona al'kur'ani, wanda babban laifi ne a Pakistan da ka iya janyo hukuncin daurin rai da rai a jarum.
An dai tsare yarinyar mai suna Rimsha mai kimanin shekaru 14 ne har na tsawon makwanni biyu a Isalamabad babban birnin kasar ta Pakistan, bayan da wasu gugun jama'a cikin fushi suka ce sai an hukunta ta, hakan kuma ya haifar da suka daga kasshen waje.
Mahaifin yarinyar ya ce yana fargabar hadarin da ke tattare da rayuwar 'yarsa da ma ta daukacin iyalansa, inda ya yi kira ga shugaban Pakistan Asif Ali Zardari da ya yi mata afuwa.
An dai killace iyayen Rimsha a wani kebabben wuri sakamakon barazanar da suke fuskanta, kana wasu iyalai kiristoci da dama da ke kusa da yankin sun tsere domin neman mafaka.
Wasu bayanai dai sun ce ana amfani da dokar mai tsauri ta aikata sabon a Pakistan wajen cimma wasu manufofi na daban, inda ko a shekaru biyun da suka gabata ma sai da aka yiwa wasu fitattun 'yan siyasa kisan gilla sakamakon sukar da suka yi game da dokar.












