
Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha
A yau ne Shugabannin kasashen Afirka, da wasu fitattun mutane ke halartar jana'izar tsohon Fira Ministan kasar Habasha Meles Zenawi.
Akalla shugabannin kasashe 20 ne da sauran fitattun mutane da suka hada da attajirin nan na kasar Amurka Bill Gates suka hallara a birnin Addis Ababa domin jana'izar.
Mr Zenawi wanda ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 21, ya rasu ne a wani asibiti a kasar Belgium a watan jiya, bayan da ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
Dubun dubatar 'yan kasar ta Habasha ne ke nuna alhinin mutuwar shugaban da suka ce ya kawo ci gaba a kasar.
Marigayi Mr Zenawi ya samu jinjina saboda irin rawar da ya taka wajen ganin tattalin arzikin kasar ya habbaka cikin gaggawa a zamaninsa, bayan tsawon lokacin da kasar ta shafe tana fama da ja'ibar yunwa.
Meles Zenawi ya kasance babban abokin Amurka, wajen yaki da ta'addanci a yankin kusurwar Afrika.
Sai dai kuma gwamnatinsa ta sha suka bisa zargin cin zarafin bil'Adama da kuma hana 'yancin kafafen watsa labarai.













