
Shugaba Muhammad Mursi na Masar
Wata mata sanye da hijabi ta karanta labarai a gidan talabijin na gwamnatin Masar.
Wannan ne dai karo na farko da hakan ta taba faruwa tun lokacin da aka kafa gidan talabijin din a shekarun 1960.
Matar ta gabatar da shirin mai suna Fatimah Nabil, ta sanya bakar kwat da hijabi mai ruwan madara.
Ta kuma fadawa BBC cewa abin da ta yi ya nuna cewa juyin-juya halin da aka yi a kasar ya kai ga gidan talabijin din na gwamnati.
Ana kuma sa ran wadansu matan da ke gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin din za su bi sahunta.
A kasar ta Masar dai akwai doka ta fatar baka wadda ta haramtawa mata masu gabatar da shirye-shirye yin lullubi a wani abin da ake ganin mataki ne na hana aiki da duk wasu alamomin addinin Islama a bainar jama'a.













