
'Yan sandan yanki na Afghanistan
Jami'an Amurka a birnin Kabul sun ce za su kirkiro wadansu sababbin matakai masu tsaurin gaske na tantance ’yan sanda a Afghanistan.
Sun kuma ce za a dakatar da horar da wadansu sababbin ’yan sanda wadanda aka dauka aiki, sannan an haramta sayar da kakin soji da na ’yan sanda.
Hakazalika ana shirin fadada amfani da sababbin matakan zuwa aikin tantance rundunar sojin kasar mai dakaru dubu dari uku da hamsin.
An kirkiro rundunar ’yan sandan ta Afghanistan mai jami’ai dubu goma sha biyar ne domin inganta tsaro a yankunan kasar masu nisa.
An dauki wannan mataki ne dai saboda karuwar ’yan sandan Afghanistan din da kan juya baya su budewa dakarun kungiyar tsaro ta NATO wuta.












