
Birnin Aleppo na kasar Syria
Gwamnatin Syria ta ce ta dakile yunkurin kai wani mummunan hari kan sansanin sojin samanta dake kusa da birnin Aleppo.
Fadan dai ya kara rincabewa a birnin na Aleppo da ma wasu biranen kasar.
Gidan Talabijin na kasar ya nuna wasu motocin da aka makare da bindigogi masu sarrafa kansu, da sauran kayayyakin da aka kwace daga yunkurin kai harin na sansanin Rasm al-Abboud.
Wannan daya daga cikin hare-hare da daman da aka kai ne a sansanin a cikin kawanakin baya bayan nan, yayinda mayaka masu goyon bayan 'yan adawa ke kokarin hana gwamnatin amfani da jiragen yaki masu saukar angulu su taimakawa dakarun da ke kasa.
Masu fafutuka sun ce kimanin mutane dari ne aka hallaka ranar Juma'a, a fadan da ake ci gaba da gwabza wa a birnin Aleppo, da wasu sassan birnin Damascus da ma wasu sassan kasar ta Syria.
Fadan na faruwa ne a yayin da Firaministan kasar Syria Wail al-Halqi ke ganawa da jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei da kuma shugaban kasar Mahmoud Ahmadinejad.
Gwanatin Syria ta ce ta dakile yunkurin kai wani mummunan hari kan sansanin sojin saman ta dake kusa da birnin Aleppo.













