
Ma'aikata masu hakar ma'adinai suna zanga-zanga
Masu shigar da kara a Afirka ta Kudu sun dakatar da tuhumar wadansu ma'aikata masu hakar ma'adinai dari biyu da saba'in.
An yi shirin tuhumar ma’aikatan ne dai da hannu a kisan abokan aikinsu talatin da hudu wadnda ’yan sanda suka harbe yayin wata zanga-zanga a watan jiya.
An kuma ce za a saki ma’aikatan cikin makwanni biyun da ke tafe.
Jama'a a kasar ta Afirka ta Kudu sun nuna rashin jin dadinsu tun farko da aka ce za a yi amfani da wata doka ta lokacin mulkin wariyar launin fata wajen tuhumar ma'aikatan da kisan abokan aikinsu, duk da cewa yawancin harbin da ya hallaka rayuka a al’amarin ya fito ne daga ’yan sanda.













