
Muhammad Al Qahtani
An soma shari'ar wani fitaccen mai fafutukar kare hakkin bil'adama na Saudi Arabia.
Shi dai Muhammad Al Qahtani yana fuskantar tuhuma da dama da suka hada da, kafa wata kungiya ba bisa ka'ida ba, da kuma amfani da kungiyoyin kasashen wajen wajen sukar hukumomin kasar, da kuma karya mubayi'arsa ga sarkin kasar.
Muhammad Al Qahtani dai shehin malamin jami'a ne da ya kware a fannin tattalin arziki.
Ya kuma fadawa BBC cewa, yana fafutuka ne domin bayyana irin zalunci da danniya da sarakun Saudiyya ke yi.
Idan dai har kotun ta same shi da laifi, to zai iya fuskantar daurin shekaru biyar a gidan kaso.













