
Shugaba Alpha Conde na Guinea
Jami'an gwamnatin Guinea sun ce akalla mutum talatin sun mutu yayin wani hadarin jirgin ruwa a tekun Atlantika.
Jirgin ruwan, wanda ya taso daga birnin Conakry za shi tsuburin Kassa, ya nutse a teku ne sakamokon iska da ruwa mai karfin gaske.
Daya daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu, Mame Asta Bangoura, ta bayyana cewa:
An yi ta iska mai karfin gaske, sai kuma injin din jirgin ya dauke wuta, amma aka ta da shi, sannan kuma ya sake mutuwa, kuma daga nan ne jirgin ya fara nutsewa.
Irin wannan hadari dai ba wani sabon abu ba ne a Guinea da ma wadansu kasashen Afirka saboda yadda ake yiwa jiragen ruwa lodin da ya wuce ka'ida.













