
Rikicin Afganistan
Wasu tagwayen bama-bamai da suka tashi kusa da wani sansanin sojoji na Nato a Afghanistan sun yi sanadiyar mutuwar akalla fararen hula tara da kuma 'yan sanda hudu.
Harin wanda aka kai a gundumar Wardak, ya kuma lalata wata kasuwa in ji jami'ai.
Wani dan tada kayar baya da ke tafe a kafa ne ya kai harin farko, sannan wata mota makare da bama-bamai ta yi bindiga.
Ana dai fargabar samun karin tashe-tashen hankula a kasar ta Afghanistan a lokacin da sojojin kasashen waje za su janye daga Afghanistan a shekarar 2014.


















