
Ana jiran jin ta bakin masu tuhuma
Lauyoyi a Afirka ta Kudu na barazanar daukar matakin shari'a a madadin mahakan ma'adinai su dari biyu da saba’in, wadanda ake zargi kisan abokan aikinsu guda talatin da hudu.
‘Yansanda ne dai suka harbe wadannan abokan aikin mahaka ma’adinan.
Lawyoyin dole ne a sako mahaka ma'adinan da ake tsare da su, nan da gobe Lahadi, ko kuma suka ce su daukaka kara zuwa babbar kotu domin ta ba da umurnin a sake su.
Ana dai tuhumar Ma'aikatan ne a karkashin wata doka ta zamanin wariyar launin fata
Joseph Mathunjwa shi ne shugaban kungiyar ma'aikatan hakar ma'adinai da gine-gine, ya kuma ce, Abin ya zo min da mamaki.
Ta yaya za ka tuhumi mutanen da ba su yi harbe mutanen da bindiga ba, wadanda kuma babu shaidar cewa sun kashe kowa, a kuma bar 'yan sanda?













