
Wani helikwaftan Syria da 'yan tawaye suka harbo
Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce ’yan tawayen Syria sun harbo wani jirgin yaki a lardin Idlib.
Tashar talabijin ta Al-Arabiya mai watsa shirye-shiryenta da Larabci ta nuna wani hoton bidiyo da ta ce yana nuna matukin jirgin, bayan ya duro daga jirgin.
Bidiyon dai ya nuna wani mutum yana saukar lema daga can nesa, yayin da mayakan ’yan tewaye ke shagalgula.
Sai dai ba a tabbatar da sahihancin hotan bidiyon ba har ya zuwa yanzu.
Gwamnatin Syria tana kara amfani da jiragen yaki wajen yakar masu yi mata bore.
A baya-bayan nan ’yan tawayen Syria sun ce sun harbo wani jirgin yaki da kuma wani jirgin helikwafta na gwamnati.













