
Masu gabatar da kara sun tuhumi masu zanga zanga da laifin kisa
Masu shigar da kara a Afrika ta kudu na tuhumar masu hakar ma'adinai da aka kama a mahakar Marikana da laifin kashe abokan aikinsu 34, wanda 'yan sanda su ka harbe.
Masu shigar da karar dai sunyi amfani da wata doka ta lokacin mulkin wariyar launin fata da ta ce, idan mutane su ka yi fito na fito da 'yan sanda kuma aka samu mutuwa ko jikkata, to wadanda aka kaman za a tuhuma da laifin aikata kisan ko da ba su ne su ka aikata ba.
Ana dai tuhumar masu hakar ma'adinai 207, biyo bayan hatsaniyar da ta barke tsakanin su da 'yan sanda saboda batun biyan albashi, abinda ya yi sanadiyyar mutuwar dan sanda guda.













