
Farashin Kayan abinci ya hau a duniya
Farashin kayan abinci a duniya ya karu da kaso goma cikin dari a watan yuli sakamakon farin da aka samu a Amurka da kuma gabashin turai.
Bankin duniya ya ce farashin kayan abinci da su ka hada da masara da alkama ya tashi da kaso ashirin da biyar cikin dari, yayinda farashin waken soya ya karu da kaso sha bakwai cikin dari.
Farashin Shinkafa ne kadai ya fadi da kaso hudu cikin dari.
Bankin duniyar ya ce tashin farashin kayayyakin abincin na barazana ga lafiya da kuma walwalar miliyoyin al'ummar duniya.













