
Dakaru a yankin Waziristan.
Dangin daya daga cikin shugabannin kungiyar Haqqani, daya daga cikin fitattun kungiyoyi masu daukar makamai a Afghanistan, ya ce an kashe shi, a sakamakon wani hari na jiragen saman yakin Amurka masu saffara kan su.
Dan uwan Badruddin Haqqani ya shaidawa BBC cewa an kashe shi ne ranar Talata, a wani harin da jirgin saman Amurka maras matuki ya kai a yankin Waziristan ta Arewa na kasar Pakistan.
Rundunar sojan Amurka dai ba ta tabbatar da kisan ba, amma idan hakan ya tabbata, masu aiko da rahotanni na cewa zai kasance babbar nasara ga dakarun Amurka a Afghanistan.
A wani lamarin na daban, wani harin da NATO ta kai ta sama, a gabashin Afghanistan, ya halaka wani kwamandan Taliban na Pakistan, Mullah Dadullah, da wasu mayaknsa sama da goma.
Amurka dai na cigaba da kai hari wasu yankunan Pakistan dake kan iyaka da Afghanistan ta hanyar amfani da jiragen sama masu sarrafa kansu.
Sai dai kuma Pakistan na cigaba da nuna rashin jin dadinta da irin wadannan hare-hare, sai dai kuma Amurka kan ce, yankunan da take kai hari suna karkashin ikon mayakan sa kai ne, ba gwamnatin Pakistan ba.













