
Rundunar 'yan sandan a Taraba dake arewa maso gabashin Nigeriya ta ce ta fara gudanar da bincike game da farar fata dan yankin Ireland da aka kashe a jihar .
'Yan sandan na sun ce, Mr Robert Gray ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da da wasu 'yan fashi suka harbe shi a hanyar Wukari zuwa Takun dake jihar ta Taraba.
Shi dai mamacin yana aiki ne da kamfanin gine-gine na PW da yake gina hanyoyi a jihohi da dama na Najeriya.
Cikin 'yan shekarun nan dai Najeriya na fuskantar karuwar matsalar tsaro.


















