
Inda ambaliya ta yi barna a Najeriya
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya jawo ambaliyar ruwa jiya a wadansu jihohi na arewacin Najeriya.
Ruwan mai karfin gaske ya sa mutane da dama sun rasa gidajensu.
Ambaliyar ruwan dai ta shafi wadansu garuruwa a jihohin Yobe da Bauchi da Jigawa.
Sai dai al’amarin ya fi kamari ne a garin Gashua dake Jihar Yobe, inda rahotanni suka ce mutane tara sun mutu, gidaje da dama kuma sun rushe.
Tun kwanaki ne dai Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta kasar ta yi hasashen cewa ruwan sama zai yawaita, musamman a wadansu jihohi a arewacin kasar.













