
Shugaban Niger, Issufou Muhammadou
Yau ne gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yi wani taro da abokan arzikinta masu hannu da shuni domin yi musu bayani game da ambaliyar ruwan da kasar ke fuskanta domin neman taimako daga wajensu.
Gwamnatin dai ta ce tana bukatar kayayyakin abinci da magunguna da tantuna da gidan sauro ko sange da kudade masu dimbin yawa domin kai dauki ga wasu 'yan kasar sama da dubu 300 da suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar.
Abokan arzikin dai sun nuna amincewarsu da su tallafa ma kasar ta nijar da abin da ya sawwaka domin taimaka wa wadanda ambaliyar ta ci.
Tuni dai gwamnatin ta ce a nata bangaren ta samar da abincin da ya kai tones dubu da dari hudu da kudade miliyan dari bakwai na CFA domin tunkarar matsalar.












