
Ban Ki-Moon
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Babban Sakatarenta, Ban Ki-Moon, zai halarci taron koli na kasashe masu tasowa 'yan ba-ruwan mu da za a yi kasar Iran cikin makon gobe duk da kiraye-kirayen da Amurka da Isra'ila ke yi masa na ka da ya halarci taron.
Kakakin Mista Ban ya ce zai yi amfani da taron ne don gabatar da damuwar da kasashen duniya ke da ita ga shirin nukiliya na kasar Iran da kuma tashin hankalin da ake yi a Syria.
Ya ce: "Sakatare Janar din ya kuma ba da muhimmanci ga hakkin da ke kansa, da Majalisar Dinkin Duniya na bin hanyoyin lumana wajen shawo kan kasashen kungiyar''.
Amurka da Isra'ila na son a mayar da Iran saniyar-ware ne saboda a cewarsu, tana kera makaman nukiliya duk da yake Iran din ta sha cewa tana kera makamashin nukiliya ne don aikin zaman lafiya.












