
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Hukumar kashe gobara ta Jamhuriyar Nijar ta yi kiyasin cewa ambaliyar ruwan da ta lashe unguwanni da dama a birnin Yamai ta raba mutum kimanin dubu hamsin da muhallinsu, yayin da aka tafka asarar dukiya mai dimbin yawa.
Ambaliyar ruwan dai ta auku ne sakamakon ruwan sama tun daga daren ranar Asabar har zuwa safiyar ranar Lahadi, al.’amarin da ya sa gidaje da dama suka rushe.
Tuni dai Firayim Ministan kasar, Malam Brigi Rafini, ya zagaya unguwannin da ambaliyar ta shafa domin ganewa idanuwansa halin da mutane suka samu kansu a ciki.
Hukumar ta kashe gobara dai ta karyata rahotannin da ke cewa mutane hudu sun rasa rayukansu tana cewa ba wanda ya rasa ransa a ambaliyar, amma Ministan Tsaron Kasa, Mouhammadou Karidjo, ya tabbatar da cewa an samu rasa rayuka, ko da yake bai bayar da alkaluma ba.
Gwamnatin Nijar din dai ta bayyana aniyarta ta tallafawa wadanda suka rasa muhallinsu.













