
Musulmi na Sallah
Ranar Lahadi Musulmi a fadin duniya suka yi bukukuwan sallar Eid el-Fitr wadda aka fi sani da karamar sallah.
Ana wadannan bukukuwan ne bayan kammala azumin watan Ramadan.
Al'ummar Musulmin a Najeriya sun bi sahun takwarorinsu da ke sauran bangarorin duniya wajen yin bikin na sallah.
Sai dai wadansu mazauna Abuja, babban birnin kasar sun yi kukan cewa bikin ya same su ne a cikin wani halin kunci, sakamakon matsalar karancin man fetur da suke fuskanta.
Akasarin gidajen man da ke birnin na Abuja dai a rufe suke, yayin da 'yan bunburutu ke sai da mai a kan farashi mai tsadar gaske.
Jiya wasu suka yi tasu sallar
Tun a jiya ne dai wadansu kasashen wadanda suka hadar da Nijar, da Pakistan, da Afghanistan suka yi tasu sallar domin, a cewarsu, sun ga wata.
A lokaci irin wannan, Musulmi kan yi kwalliya su je Sallar Idi domin raka'a biyu ta nafila.
Bayan nan ne kuma suke ci gaba da taya juna murna ta hanyar ziyarce-ziyarce da kuma wadansu nau'o’in nishadi.













