
Julian Assange
Julian Assange, wanda ya kafa shafin nan na Internet mai kwarmata bayanai, ya fito bainar jama'a karon farko cikin watanni biyu.
Yayi jawabi ne daga tagar benan ofishin jakandancin Ecuador dake nan birnin London, inda ya fake domin gujewa tusa keyarsa zuwa Sweden domin fuskantar zargin kokarin yin lalata da wasu mata.
Yayin jawabinsa, Julian Assange yayi wani kira ga shugaba Obama na Amurka, inda yace, 'ina kira ga shugaba Obama yayi abinda ya dace, Amurka ta dakatar da bi-ta-da-kullin da take yiwa shafin Wikeleaks.'
Birtaniya dai ta dage cewa, tana da ikon kama shi, kuma lamarin ya haifar da tankiya tsakaninta da Ecuador.













