
Gidajen da ambaliyar ruwa ta share a arewacin Najeriya
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa a Jihar Legas da ke Najeriya ta ce tana can tana neman wadansu mutane goma sha biyar wadanda suka bata bayan wata igiyar teku ta yi awon gaba da su.
Akalla mutun daya ya mutu bayan da igiyar tekun ta afkawa al'ummomin da ke zaune a unguwar Kuramo Beach dake gabar tekun Atlantika a birnin na Legas.
A daren ranar Juma’a ne dai igiyar ruwan ta mamayi unguwar ta marasa galihu lokacin da mutane ke barci.
Shugaban hukumar, Olufemi Oke, ya shaidawa BBC sun killace wurin, sannan ya kara da cewa:
Da faruwar al’amarin, sai muka tayar da dukkan na’urorinmu na bayar da agajin gaggawa, kuma dukkan wanda ke da ruwa datsaki a al’amarin yana wurin.













