
Shugaba Muhammad Mursi na Masar
Kafofin yada labarai na gwamnatin Masar sun ce Shugaba Muhammad Mursi zai kai wata ziyara Iran a karshen wannan watan.
Wannan ce dai ziyara ta farko a cikin shekaru fiye da talatin da wani shugaban kasar Masar zai kai kasar ta Iran.
Yayin ziyarar zai halarci wani taron Kungiyar Kasashe ’yan Ba-ruwanmu, inda Masar za ta mikawa Iran shugabancin kungiyar mai kewayawa.
A shekarar 1979 kasashen biyu suka yanke hulda bayan bayan Masar ta amince da kafuwar kasar Isra’ila an kuma yi juyin juya-hali a Iran.
Masu aiko da rahotanni sun ce ana sa ran Mista Mursi, wanda mai kishin addinin Islama ne, zai yi yunkurin gyara dangantakar ksashen; sai dai kuma kasashen Yamma za su yi daridari da duk wani mataki na inganta dangantakar.


















