
Mawakan kungiyar Pussy Riot
Wata Kotu a Moscow ta sami mawakan nan Uku mata na 'Pussy Riot' da laifin dabanci.
A wata shari'a data fi jan hankalin jama'a da dama a cikin 'yan shekarun nan a Kasar Rashan, Mai shari'a Marina Syrova tace kiyayya ce ta addini da siyasa ta tunzura su, suka aikata laifin.
Tace bayan kotu ta saurari hujjojin wadanda ake zargi da kuma shaidu da wadanda abin ya shafa, sannan da yin nazari akan duk wasu abubuwa dake da alaka da shari'ar, kotu ta sami ku da aikata laifi
Tun cikin watan Maris ne dai matan suke a cikin kurkuku, bayan da suka rera wata waka ta sukar Shugaba Vladimir Putin a cikin watan Fabrariru.
Ana tsammanin za a yanke wa matan hukunci nan bada jimawa ba












