
Dalibai a Chile
'Yan sanda a Chile sun tsare mutane dari da talatin da tara, mafi yawansu matasa, wadanda suka mamaye makarantu uku a Santiago, babban birnin kasar domin nuna rashin amincewa da manufofin ilimi na kasar.
Daliban da magoya bayan su sun yi taho-mu-gama da 'yan sandan a lokacin da suka je kama su.
Wakilin BBC yace farmakin da magajin garin mai ra'ayin mazan jiya ya bada umarnin kaiwa, alama ce da ke nuna cewa mahukunta sun fara daukar tsauraran matakai akan daliban da suka dara shekara guda suna gwagwarmayar yiwa tsarin ilimin kasar garambawul.
Akwai dai yiwuwar rikici sosai matsawar 'yan sandan suka sake matsin lamba ga daliban.


















