
Mutane goma sha takwas ne suka mutu sakamakon arangamar
'Yan sandan Afurka ta kudu sun budewa ma'aikatan wuraren hakar ma'adinai wuta yayin wani artabu dangane da bukatar karin albashi.
Rahotanni dai na cewa, an ga gawarwaki kusan sha takwas a bakin wurin hakar ma'adinai na Lonmin dake da nisan kusan kilomita dari daga babban birnin kasar Johannesburg.
A waje daya kuma kafofin yada labarun Afrika ta Kudu sun ce arangamar tsakanin 'yan sanda da ma'aikatan hakar ma'adinan dake zanga-zanga ta kai ga hallaka mutane goma sha biyu.
Wani mutum da ya ganewa idansa abin da ya faru mai suna Molaole Montsho ya shaidawa BBC cewar " 'yan sandan sun nemi masu zanga zangar da su a jiye makamansu su kuma bar wajan, amma suka ki".
Tun daga ranar Juma'ar data gabata ma, an kashe mutane goma da suka hada da 'yan sanda biyu a wurin hakar ma'adinan sakamakon sa-in-sa ta cikin gida tsakanin kungiyoyin kwadagon dake gaba da juna.
Hukumomi a kasar sun ce zanga-zangar ta sabawa doka.












