
birnin Lagos
Kungiyar 'yan jarida ta kasa reshen jihar Lagos a Nijeriya, ta gudanar da wata zanga zangar lumana a yau Alhamis, tana korafin ana cin zarafin 'ya'yanta.
A farkon makon nan ne aka lakada ma wasu 'yan jarida duka, bayan da suka dauki hoton wasu da suke satar hawa kan jiragen kasa.
Ana dai zargin wasu zauna-gari banza ne da kai masu wannan hari.
Ko a makon jiya wasu ma'aikatan dakin ajiye gawa na wani asibitin Lagos din sun daki wani dan jarida suka yi masa rauni.
Hakan na faruwa, bayan da a watan jiya wani dan jaridar, Razak Gawat ya bace, kuma har yanzu ba a ji duriyarsa ba.
Kungiyar 'yan jaridar ta mika kokenta ga gwamnatin jihar Lagos, tana neman a dauki matakan kare 'yan jarida daga irin wannan cin zarafi.
Ko a jiya, Laraba, shugaban 'yan jaridar na kasa a Nijeriya, Malam Muhammad Garba, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta samar da wani tsari da zai ba 'yan jaridar gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba.












