BBC navigation

Ana kara ta da jijiyoyin wuya a kan Assange

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 12:10 GMT

Rafael Correa, Shugaban Ecuador

Ana kara tayar da jijiyoyin wuya a kan makomar mtumin da ya kirkiri shafin nan mai kwarmata bayanai a intanet, Julian Assange, sa'o'i kadan kafin kasar Ecuador ta bayar da sanarwa a kan ko za ta ba shi mafaka.

Birtaniya ta ce tana iya baiwa ’yan sandanta hurumin shiga ofishin jakadancin kasar ta Ecuador da ke London su kama Mista Assange.

Mista Assange ya buya a ofishin jakadancin ne don gudun mika shi ga hukumomin Sweden.

Ecuador dai ta yi Allah-wadai da yunkurin baiwa ’yan sanda shiga ofoshin, tana cewa kutsa kai ciki keta yarjejeniyar diflomasiyya ce ta kasa-da-kasa.

Birtaniya ta kuma ce ba za ta lamince wa Mista Assange ya fice daga ofishin jakadancin ba idan Ecuador ta ba shi mafaka.

Ana neman Mista Assange a Sweden ne don ya amsa tambayoyi a kan wadansu lafuffukan da suka shafi jima'i.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.