
Julian Assange da ake cacar baki akansa
Ecuador ta baiwa mutumin da ya kirkiri shafin intanet mai kwarmata bayanai na Wikileaks, Julian Assange, mafakar siyasa, tana cewa yana fuskantar hadarin za a musguna masa.
Watan Mista Assange biyu ke nan a ofishin jakadancin kasar ta Ecuador da ke London a yunkurinsa na gujewa amsa tambayoyi dangane da zargin aikata laifuffukan da suka shafi lalata a Sweden.
Ministan harkokin wajen Ecuardo, Ricardo Patiño, ya ce akwai fargabar za a mika Mista Assange din ga Amurka daga Sweden, inda za a tuhume shi da bankada wadansu sakwannin sirri na diflomasiyya.
Mista Patiño ya bukaci Birtaniya ta kyale Mista Assange ya fice daga kasar, amma tuni gwamnatin kasar ta Birtaniya ta ce ba za ta sabu ba, tana bayyana shawarar da Ecuador ta yanke da cewa abin takaici ne.
Sweden ma ta yi watsi da damuwar da Ecuador ke nunawa.


















