
tunisia women protest
Dubun dubatar mata a Tunisia na zanga-zanga a Tunis babban birnin kasar, domin nuna adawa da matakin
da gwamnatin ta dauka na cewa wani sashe na sabon kundin tsarin mulkin da yanzu haka ake rubutawa, wanda jam'iyyar Ennahda ke goyon baya, na yin karan tsaye ga hakkin mata.
Zanga-zanga na ci gaba da kara karfi a Tunisia ne kan abin da wasu ke yi wa kallon matakan takaita 'yancin mata ne daga jam'iyyar 'yan ra'ayin Musulunci wadda ta yi nasara a zabe, bayan faduwar gwamnatin Zine El Abidine Ben Ali da ya dade yana mulkin kasar.
Gwamnatin ta fitar da daftarin doka da ke nuni da mata a matsayin mataimaka,maimakon daidai da maza.
Akasarin matan masu zanga-zanga sun daga kwalaye sama da aka rubuta ''mata ku tashi ku nemi yancinku.''
Kundin tsarin mulkin kasar ta Tunisia na shekarar 1956 ya tanadi cewa mata da maza daidai suke, ya kuma hana auren mace fiye da daya.













