
Ana ayyukan ceto a inda jiragen Uganda suka yi hatsari
An gano jirage masu saukar ungulu guda biyu na kasar Uganda da suka yi hatsari a wani surkukin yanki na kenya, bayan sun bace ranar Lahadi, a cewar jami'ai a Kenya.
An gano jiragen ne a kan wani tsauni, wanda shi ne na biyu mafi tsawo a nahiyar Afrika.
Jami'an sun kuma bayyana cewa an sami gawawwakin mutane biyu, yayin da sauran mutane takwas dake jiragen an samu ceto su da rai.
Duka jiragen yakin biyu an tura su ne zuwa Somalia domin karfafa dakarun kungiyar Tarayyar Afrika wato AU dake Somaliya.
Jirgi mai saukar ungulu na ukun da aka tura ya yi saukar gaggawa a wani tsauni a Kenya ranar Lahadi.
Haka kuma kakakin rundunar sojin Kenya, Cyrus Oguna ya ce an ceto fasinjojin dake jirgin baki daya.
Jirgi mai saukar ungulu daya ne kawai ya tsaya a Garissa a kasar Kenya domin shan mai a kan hanyarsa ta zuwa Somalia cikin jirage hudun da aka tura.












