
Shugaba Morsi na Masar
Wata kotu a Masar ta yankewa wasu musulmi 'yan bindiga su goma sha hudu hukuncin kisa saboda samun su da laifin kai hari bara a arewacin Sinai, inda 'yan sanda da dama suka mutu.
An kuma tuhumi mutanen da kirkirar wata haramtaciyyar kungiya mai suna Al Tawheed wa al Jihad.
Hukuncin na zuwa ne bayan wani hari da ake zargin musulmi ne suka kai a makon daya gabata a yankin na Sinai, inda jami'an tsaro goma sha shida suka hallaka.
Shugaban Kasar Masar Mohammed Morsi ya aiwatar da garambawul a rundunar sojin Kasar bayan harin.
A halin da ake ciki Amurka ta ce zata ci gaba da aiki da shugabannin kasar ta Masar, fararen hula da kuma sojojin.
Ranar Lahadi ne sabon shugaban kasar ta Masar, Mohammed Morsi ya kori ministan tsaron kasar , mai karfin fada-aji, Fil Mashal Hussein Tantawi, wanda ya rike ragamar mulkin kasar, har zuwa zaben
da aka gudanar, tun daga faduwar gwamnatin shugaba Hosni Mubarak.













