
Hassan Nasrallah shugaban Hezbollah
Amurka ta zargi kungiyar 'yan bindiga ta Hezbollah da ke Lebanon da laifin ba da horo tare da shawarwari ga gwamnatin Syria a kokarinta na murkushe boren 'yan adawa da karfin soji.
Haka kuma ta zargi Hezbollah din da tallafawa dakarun juyin juya halin Iran wurin baiwa sojin Syria horo.
Amurka dai ta dade da baiyana Hezbollah a matsayin kungiyar ta'addanci kuma yanzu ta sake sanar da karin takunkumi a kanta.
wakilin BBC a Washington ya ce sabon takunkumin ba shi da wani tasiri kasancewar kungiyar ba ta da wata kadara a Amurka.













