bbc.co.uk navigation

Girgizar kasa ta hallaka mutane 180 a Iran

An sabunta: 11 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:27 GMT
Wata girgizar kasa a Iran a 2005

Wata girgizar kasa a Iran a 2005

Girgizar kasa mai karfi ta jijjiga arewa maso yammacin Iran har sau biyu ba kakkautawa.

Jami’ai sun ce akalla mutane dari da tamanin sun rasa rayukansu yayin da fiye da dubu da dari uku suka jikkata.

An bayar da rahoton cewa girgizar kasar ta katse duk wadansu hanyoyin sadarwa da yankin wanda ke kusa da birnin Tabriz, al'amarin da ya sa hukumomi ke shan wahala wajen tantance barnar da ta auku.

Amma dai wani jami'i a yankin ya shaidawa BBC cewa girgizar kasar ta yi mummunar barna ga kauyuka kusan sittin.

Girgizar kasar mai karfin maki shida da digo hudu da kuma maki shida da digo uku ta haddasa daukewar wutar lantarki a galibin birnin Tabriz.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

  • ,

BBC © 2013 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.