BBC navigation

An bude majalisar Kenya mai kujera daya dala 3,000

An sabunta: 7 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:24 GMT
kujerun majalisar kenya

Sababbin kujerun Majalisar Kenya

Shugaban kasar ta Kenya Moi Kibaki shi ne ya jagoranci bikin bude ginin majalisar wanda aka gyara tare da sakewa fasali da kayayyakin kawa da na zamani.

Ba al'ummar kasar kadai ba hatta su kansu wasu daga cikin 'yan majalisar sun nuna rashin amincewarsu tare da ja akan aikin gyaran majalisar tun da farko.

A da dai an baiwa wani kamfanin kasar waje ne kwangilar samarda sabbin kujerun majalisar to amma bayanda wasu daga cikin 'yan majalisar suka gano cewa kowacce kujera zata tashi akan dala dubu 5 sai suka tada kayar baya abin da ya sa aka soke wannan kwangila, aka baiwa hukumar kula da gidajen yari ta kasar aikin inda ita kuma ta yi kujerun 350 akan dala dubu 3 kowacce
daya.

Hukumomin kasar sun ce aikin gyaran ginin majalisar da aka yi wanda aka kashe dala miliyan 12 ya sa komai na ginin majalisar ya zama na zamani musamman ma kayayyaki da na'urorin sadarwa kuma hakan zai sa a samu cigaba a ayyukan majalisar kamar yadda shugabanta Kenneth Marende ya shedawa BBC.

Yace tsarin kuri'a da ake da shi yanzu inda dan majalisa zai latsa wani abu kawai ba kamar a da ba zai bashi damar bayyana matsayinsa a duk lokacin da ake neman kuri'a ba tare da wani shugabansa a majalisa ya yi masa katsalandan ko tilasta masa zaben abin da ba shi ya yi niyya ba.

Tsadar Kujeru

"Ban ga dalilin da zai sa 'yan majalisa su zauna akan kujerar dala dubu 5 ba kudin da zai iya gina duk wani dan karamin gida da ake bukata."

John Mbadi dan kwamitin kudi na majalisar Kenya

Ya ce yanzu kowana dan majalisa ya sami 'yancin kansa inda zai danna wani abu kawai a inda yake zaune a san matsayinsa ba tare da wata hayaniya ko bata lokaci ba.

Game da sababbin kujerun kuwa wakilin BBC a babban birnin kasar ta Kenya Nairobi yace wasu 'yan kasar na kokawa da cewa kujerun ne suka fi tsada tsakanin dukkanin kujerun majalisun kasashen kungiyar Commonwealth.

Aikin gyaran ginin majalisar da aka fara a watan Afrilu na 2010 da kuma aka tsara kammala shi cikin shekara daya an jinkirta shi saboda ce-ce-ku-cen da aka yi ta yi a kansa game da yawan kudin da za a kashe da kuma yanayin bada kwangilar.

Mr John Mbadi dan kwamitin kula da sarrafa kudaden gwamnati na majalisar shi ne kan gaba wajen adawa da tsarin tun farko inda ya ce shi bai ga dalilin da zai sa 'yan majalisa su zauna akan kujerar dala dubu 5 ba kudin da zai iya gina duk wani dan karamin gida da ake bukata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.