BBC navigation

Koriya ta Arewa ta sallami shugaban sojinta

An sabunta: 16 ga Yuli, 2012 - An wallafa a 07:13 GMT

Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim da Ri

Kafafen yada labarai na Koriya ta Arewa sun ce an cire shugaban sojin kasar daga dukkan mukamansa na soji da kuma na siyasa.

Rahotanni sun ce an cire Ri Yong-Ho daga bakin aikinsa ne saboda rashin lafiya sai dai wakilin BBC yace masu lura da al'amura na zargin akwai lauje cikin nadi.

Ana dai ganin Mr Ri ne a matsayin wani kusa a shirin mika mulki ga shugaba mai ci, Kim Jung-un.

Wakilin BBC na cewa salon mulkin sabon shugaban ya sa mutane da dama na ganin yiwuwar samun sauye-sauye a kasar mai bin tsarin Makisanci samfurin tsohon shugaban Soviet Joseph Stalin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.