BBC navigation

Shugaban bankin Barclays na Birtaniya ya yi murabus

An sabunta: 3 ga Yuli, 2012 - An wallafa a 15:57 GMT
Bob Diamond

Bob Diamond

Shugaban gudanar da katafaren bankin Barclays na Birtaniya, Bob Diamond ya yi murabus bayan sukan da ya sha akan zargin da aka yi wa bankin na yin cogen kudin ruwa.

Bankin Barclays dai ya fuskanci suka tun bayan da ya amsa cewar ya yi kokarin yin coge wajen saka kudin ruwa da bankin ke cazar wasu bankunan, ko yake biya.

A jiya ma shugaban hukumar gudanarwar bankin Marcus Agius , ya sauka daga kan mukaminsa.

BBC dai ta gano cewa, Bob Diamond ya yanke shawarar yin murabus ne bayan gwamnan babban bankin Ingila, Sir Mervyn King da kuma shugaban hukumar dake sa ido akan cibiyoyin kudi na Birtaniya, Lord Turner sun ce masa abinda ya kamata shi ne, ya yi murabus.

Wakilin BBC ya ce, shi dai Bob Diamond ya ce, akwai siyasa a cikin matsin lambar da aka yi masa yayi murabus, kuma tuni 'yan siyasa ke yin marhabun da yin murabus din da yayi.

Bob Diamond dai ya ce, matsin lamba a kan wannan batu ka iya yin illa ga bankin na Barcklays.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.