BBC navigation

Cyprus ta bukaci tallafin kudi daga Turai

An sabunta: 25 ga Yuni, 2012 - An wallafa a 20:21 GMT
Shugaban Cyprus Dimitiris Christofias da Kwamishinan Fadada Tarayyar Turai Stefan Fule

Shugaban Cyprus Dimitiris Christofias (a dama) da Kwamishinan Fadada Tarayyar Turai Stefan Fule

Kasar Cyprus ta bukaci kungiyar Tarrayar Turai ta samar mata da kudi don ceto tattalin arzikinta.

Gwamnatin kasar ta Cyprus ta ce bankunanta na fama da matsaloli saboda dinbim basussukan da suke bi a kasar Girka.

Rahotanni sun nuna cewa banki na biyu mafi girma a Cyprus na bukatar tallafin gaggawa.

Wani masanin tattalin arziki, Justin Urquhart, ya bayyana cewa:

“Ba na tunani za a ba su bashin ba tare da wadansu sharudda ba, saboda alakarsu da Girka, kuma ba a so a fara nuna bambamci a cikin lamarin”.

Kasar ta Cyprus dai ta kasance kasa ta biyar dake amfani da kudin Euro da ta bukaci tallafi don ceto tattalin arzikinta, bayan kasashen Jamhuriyar Ireland, da Portugal da Girka da kuma Spain.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.