
Masu zanga-zanga a Masar
Al'ummar kasar Masar suna kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben sabon Shugaban kasa wanda zai gaji Hosni Mubarak da aka hambaras bara.
Ana hasashen za a yi kankankan ne tsakanin 'yan takara biyu2 da suka rage tsohon Prime Minista Ahmed Shafiq da Mohammed Morsi na jam'iyyar Muslim Brotherhood.
Sojojin dake jan ragamar mulkin kasar a yanzu sun yi alkawarin mika mulki ga wanda ya yi nasara.
A dandalin Tahrir dake tsakiyar birnin Alkahira masu zanga-zanga na cigaba da hallara don nuna bacin-ransu, suna kalaman batanci ga gwamnatin mulkin sojin ta Masar.













