BBC navigation

Babu wanda ya tsira a hadarin jirgi a Pakistan

An sabunta: 20 ga Aprilu, 2012 - An wallafa a 19:08 GMT
Hadarin jirgi a Pakistan

Hadarin jirgi a Pakistan

Wani jirgin saman fasinja dauke da sama da mutane dari da ashirin, ya fadi a kusa da Islamabad, babban birnin kasar Pakistan.

'Yan dakikoki kadan ya rage jirgin ya sauka a lokacin da akai ta tsawa.

Wadanda suka ga abin da ya faru sun ce jirgin ya kama da wuta lokacin da ya daki kasa a kusa da wata unguwa.

Jirgin, kirar Boeing 737, mallakar kamfanin jiragen sama na kasar ta Pakistan wato Bhoja Air kuma ya taso ne daga Karachi.

Wani dan sanda ya ce gaba daya jirgin ya tsarwatse kuma ba yadda za'ai a samu wani a cikin jirgin da rai.

A watan jiya ne kamfanin jiragen saman na Bhoja Air ya koma aiki bayan da a baya ya rufe sabilida matsalolin rashin kudi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.