BBC navigation

Syria ba ta mutunta shirin zaman lafiya —Ban

An sabunta: 19 ga Aprilu, 2012 - An wallafa a 08:32 GMT
Ban Ki-moon

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya ce Syria ba ta kammala sauke nauyin da ke kanta ba na janye dakarunta daga wuraren da farar hula ke zaune.

A wani rahoto da ya aike ga Kwamitin Sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya, Mista Ban ya ce ko kusa ko alama Syria ba ta nuna alamun za ta mutunta shirin samar da zaman lafiya na Kofi Annan ba—wanda ya tanadi cewa gwamnatin Bashar al-Assad ta janye dakaru da manyan makaman da ta jibge a wadansu birane da garuruwan kasar ta Syria.

Mista Ban ya ce rahotannin munanan tashe-tashen hankula da jikkata sun karu a ’yan kawanakin nan, yayin da ake ci gaba da samun rahotannin da ke nuna cewa dakarun gwamnati na yin luguden wuta a kan yankunan fararen hula.

Sakatare-Janar din ya kara da gargadin cewa wajibi ne Shugaba Assad ya cika alkawarin da ya dauka na mayar da dakarunsa bariki da kuma dakatar da bude wuta a kan al'ummar da ba su ji ba ba su gani ba.

Jami'an diflomasiyya a Kwamitin Sulhun mai mambobi goma sha biyar sun ce rahoton na Mista Ban—da ma jawabin mataimakin wakilin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Larabawa ga Syria—za su taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawara a kan ko yanayi ya yi daidai don aikewa da masu sa ido na Majalisar zuwa kasar ta Syria.

Masu sa idon su dari uku ne dai za su tabbatar da cewa ana aiki da tanade-tanaden shirin samar da zaman lafiyar.

Rahoton na Mista Ban ya zo ne kuma bayan da Kwamitin Sulhun ya amince da wani kuduri ranar Asabar wanda ya bukaci a aike da jami'an soji wadanda ba sa dauke da makamai don su sa ido a kan halin da ake ciki a kasar ta Syria.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.