BBC navigation

Yaki na ruruwa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

An sabunta: 18 ga Aprilu, 2012 - An wallafa a 19:32 GMT
albashir

Shugaban Sudan Omar Al Bashir

Sudan da Sudan ta Kudu na dada sarkewa - har ma ana fargabar yaki zai barke tsakaninsu - yayin da shugaban Sudan, Omar al Bashir, ya ce yana son ya 'yantar da al'ummar Sudan ta Kudu daga gwamnatinsu.

Kalaman da yayi a lokacin wani taron gangami a birnin Khartoum, sun zo ne bayan an kwashe kwana da kwanaki ana gwabza fada a iyakar kasashen biyu.

A cewar Shugaba Omar Al bashir na Sudan ya yi kuskuren baiwa kungiyar Sudan Peoples Liberation Movement mulki a Juba.

Fada tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu na kara yaduwa zuwa wasu yankunan dake kan iyakar kasashen biyu, abinda ke nuna tamkar alama ce ta gagarumin yaki tsakanin kasashen biyu.

Jakadan Birtaniya a Sudan, Nicolas Kay ya bayyana Allah wadai a zahiri akan mamayen da Sudan ta Kudu tayi a Heglig.

Anata bangaren kuwa, jakadar Amurka a majalisar dinkin duniya Susan Rice cewa tayi kasashen biyu sun rutsa kansu cikin tashin hankali kuma kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na duba yiwuwar kakaba musu takunkumi ta yadda zasu daina fada.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.